Skip to main content

Sabuwar Kwayar Korona Ta Bulla A Najeriya

A halin yanzu da duniya ke tsakiyar fargaba da rashin sanin makoma, Hukumar Yaki Da Cuta Mai Yaduwa ta NCDC da ke Najeriya, ta fitar da sanarwar barkewar sabon nau'in cutar annobar korona da aka lakabawa suna B.1.1.7.
Wannan sabuwar kwayar cutar dai ta fi ta farko saurin yaduwa da matukar hadari wajen kashe mutane, da aka tabbatar da ta kan yadu da kashi 70 cikin dari fiye da na farkon.
A watan Disamban 2020 aka samu rahoton bullar sabuwar koronar a kasar Burtaniya da Afirka ta Kudu.
Shugaban hukumar NCDC ta kasa Chikwe Ihekweazu ya sanar da hakan a jiya.
Ya bayyana cewa hukumar za ta kara azama don yin kandagarkin bazuwar sabon nau'in korona na B.1.1.7 tsakanin jama'a.
Wani kwararren likitan Firaministan Burtaniya Boris Johnson mai suna Patrick Vallance, ya bayyana cewa, "daga marasa lafiya 'yan tsakanin shekaru 60 zuwa sama da suka harbu da tsohuwar kwayar cutar a kasar, 10 kan rasa rayukansu a cikin mutum 1000 kowace rana, amma a wannan karon, da wannan sabon samfurin ya bulla adadin ya karu ya daga 13 zuwa 14".
Gwamnatin Najeriya dai ta bi sahun wasu kasashen duniya wajen shirin kaddamar da shirin allurar rigakafin cutar, duk da al'ummar duniya na jefa shakku game da asalin cutar kan ta da ma rigakafin da kamfunnan Moderna, Pfizer da Bio-NTech suka samar.

Comments