(Gaskiya ɗaci gareta) DALILAN DAKE SANYA TALAKA CI GABA DA ZAMA CIKIN TALAUCI, ATTAJIRI YA CI GABA DA ZAMA CIKIN ARZIKI A shekarar 2007, wani hasashe da ofishin mai kula da hada-hadar kudi na al'ummar ƙasar Amurka (Congressional Budget Office) yayi cewar, duk wasu tsare-tsare da gwamnatoci ke aiwatar wa 'yan ƙasa, attajirai kurum yafi amfana, domin kuwa talakawa na ƙara ci gaba da zamowar su cikin talauci ne kawai. Ga kaɗan daga abinda binciken su ya nuna; TALAKAWA: A tsawon shekaru talatin, samun kuɗinsu ya haɓaka ne da kaso goma sha takwas kacal. (Ma'ana talakan da yake samun dalar Amurka ɗaya a tsawon wancan lokaci, har yanzu baya samun dala biyu) MATSAKAITA: A tsawon shekaru talatin, samun kuɗin matsakaitan mutane ya ƙaru ne da kashi 40 kacal. ATTAJIRAI: A tsawon shekaru talatin, samun kuɗin attajirai ya haɓaka ninkin-ba-ninkin da kashi 275. (wannan labari na da matuƙar kyau idan aka haɗa shi da yanayin da talakawan Najeriya suke ciki daga shekaru talatin ...