Skip to main content

Posts

Showing posts from April 19, 2023

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta É—auka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na Æ™asa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaÉ“en jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naÉ—a kwamishinonin zaÉ“e domin É—aukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaÉ“en ya ayyana A'ishatu ÆŠahiru Binani a matsayin wadda aka zaÉ“a gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.