Skip to main content

Posts

Showing posts from February 7, 2023

PDP Na Shirin Korar Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya shigar da ƙara domin hana wani sabon yunƙurin jam’iyyar PDP dakatar da shi daga cikinta, kuma ya buƙaci kotun da ta ɗauki mataki ga duk masu wannan aniya.  Ɗaya daga cikin jigajigan jam'iyyar PDP da suka mayar da martani kan ƙarar da gwamna Wike ya shigar, Mahdi Shehu, ya mayar da martani a ranar Litinin da ta gabata inda ya wallafa a shafinsa na twitter wata sanarwa cewa, “Wike ya shigar da ƙara kan jam’iyyar PDP mai lamba FHC/ABJ/CS/139/2023 ta hannun lauyoyinsa, DY Musa (SAN);  Douglas Moru, da C. C. Chibuike, yana neman a ba shi umarnin hana a kore shi daga PDP.”   Wike dai ya yi ta famar ruguza jam’iyyar har ma ya rasa inda za shi. Gwamnan na Ribas ya zamewa jam'iyyar PDP ƙadangaren bakin tulu, irin yadda ya ke uwa da makarbiya tun bayan da dangantaka ta soma tsami tsakaninsa da wasu jigajigan jam'iyyar ciki kuwa har da gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.  

Japan Ƙasar Da Kowa Tsoho

A ƙasar Japan da ke gabashin Asiya, adadin haihuwa a shekara ya ragu zuwa kasa da dubu 800 a karon farko a shekarar 2022. Ya zuwa farkon shekarar 2023, kashi 29 na al'ummar Japan mai mutane miliyan 124.77 na da shekaru 65 ne ko sama da haka, kuma kashi 11.6 na tsakanin shekarun 0 da 14. Japan ita ce ƙasa ta farko a duniya bisa ga jimillar yawan jama'a masu shekaru 65 zuwa sama. Firaministan ƙasar, Kishida Fumio ya sanar da cewa Japan na gab da rasa ayyukanta na zamantakewar al’umma sakamakon raguwar yawan haihuwa kuma a bana za su mai da hankali kan manufofin renon yara. Hukumar Kula da Yara da Iyali, mai alaƙa da gwamnatin ƙasar za ta fara aiki a watan Afrilu. Kisida ya bayyana cewa suna shirin ruɓanya kasafin kuɗin manufofin da suka wajaba daga yanzu zuwa watan Yuni. Duk da ci gaban da ƙasar Japan ke da shi a fannonin ƙere-ƙere da fasaha, rashin wadattatun matasa ya sa tana fuskantar matuƙar barazana ga ƙarewar jama'a.