Skip to main content

PDP Na Shirin Korar Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya shigar da ƙara domin hana wani sabon yunƙurin jam’iyyar PDP dakatar da shi daga cikinta, kuma ya buƙaci kotun da ta ɗauki mataki ga duk masu wannan aniya.
 Ɗaya daga cikin jigajigan jam'iyyar PDP da suka mayar da martani kan ƙarar da gwamna Wike ya shigar, Mahdi Shehu, ya mayar da martani a ranar Litinin da ta gabata inda ya wallafa a shafinsa na twitter wata sanarwa cewa, “Wike ya shigar da ƙara kan jam’iyyar PDP mai lamba FHC/ABJ/CS/139/2023 ta hannun lauyoyinsa, DY Musa (SAN);  Douglas Moru, da C. C. Chibuike, yana neman a ba shi umarnin hana a kore shi daga PDP.”  
Wike dai ya yi ta famar ruguza jam’iyyar har ma ya rasa inda za shi.
Gwamnan na Ribas ya zamewa jam'iyyar PDP ƙadangaren bakin tulu, irin yadda ya ke uwa da makarbiya tun bayan da dangantaka ta soma tsami tsakaninsa da wasu jigajigan jam'iyyar ciki kuwa har da gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
 

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey