A ƙasar Japan da ke gabashin Asiya, adadin haihuwa a shekara ya ragu zuwa kasa da dubu 800 a karon farko a shekarar 2022.
Ya zuwa farkon shekarar 2023, kashi 29 na al'ummar Japan mai mutane miliyan 124.77 na da shekaru 65 ne ko sama da haka, kuma kashi 11.6 na tsakanin shekarun 0 da 14.
Japan ita ce ƙasa ta farko a duniya bisa ga jimillar yawan jama'a masu shekaru 65 zuwa sama.
Firaministan ƙasar, Kishida Fumio ya sanar da cewa Japan na gab da rasa ayyukanta na zamantakewar al’umma sakamakon raguwar yawan haihuwa kuma a bana za su mai da hankali kan manufofin renon yara.
Hukumar Kula da Yara da Iyali, mai alaƙa da gwamnatin ƙasar za ta fara aiki a watan Afrilu.Kisida ya bayyana cewa suna shirin ruɓanya kasafin kuɗin manufofin da suka wajaba daga yanzu zuwa watan Yuni.
Duk da ci gaban da ƙasar Japan ke da shi a fannonin ƙere-ƙere da fasaha, rashin wadattatun matasa ya sa tana fuskantar matuƙar barazana ga ƙarewar jama'a.
Comments