Skip to main content

Posts

Showing posts from August 9, 2022

Jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI Sun Kai Samame Gidan Dold Trump

  Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa tawagar jami’an hukumar sun mamaye gidansa na alfarma da aka fi sani da suna Ma-a-Lago da ke a gaɓar tekun jahar Fulorida. Rahotanni sun nunar da cewa samamen na da nasaba da wani bincike da ake kan gudanarwa da ke zargin Mista Trump da riƙe wasu muhimman takardun gwamanati tun bayan saukar sa daga mulki. Sai dai Mista Trump ya bayyana wannan mataki da kutsen da ya saɓawa doka, “Babu wani abu makamancin wannan da ya taɓa faruwa da Shugaban Amurka a tarihance”. Sashen adana bayanan gwamnatin Amurka ya sanar tun a farko cewa, Mista Trump bai miƙa wasu muhimman takardu ba da suka haɗa da wasiƙu da ya zama wajibi duk shugaban ƙasa mai barin gado ya hannunta bayan barin sa mulki. Jami’an ofishin sun ce sun gano manyan akwatuna 15 a gidan waɗanda ke ɗauke da muhimman takardun. Daga baya sashen adana bayanan ya shaidawa majalisar dokokin Amurka cewa kowace akwati da aka gano an yi mata a...