Skip to main content

Posts

Showing posts from September 12, 2026

Dan’iya ya nuna damuwa tare da goyon bayan kalaman Amnesty International kan karuwar ta’addanci a jihar Sokoto

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a Jihar Sokoto, Hon. Manir Muhammad Dan’iya, ya bayyana damuwa matuƙa kan ƙara yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a fadin jihar, inda ya goyi bayan kiran da Ƙungiyar Ƙare Haƙƙin Ɗan adam ta Amnesty International ta yi na gaggauta ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Dan’iya ya ce, "rahotannin da ke nuna yadda al’ummomi ke faɗawa cikin tashin hankali har ta kai suna barin garuruwansu da 'yan bindiga ke ƙonewa, tare da yin garkuwa da mata da ‘yan mata, sun nuna cewa matsalar tsaro ta kai matakin mai matuƙar muni da ke buƙatar haɗin gwiwar gwamnatin jihar da ta tarayya domin magance ta. Ya bayar da misalin yadda 'yan bindiga suka afkawa mazauna ƙauyuka da dama da suka haɗa da Girkau da Romon Liman da Romon Sarki da Margai abin da ya tilasta wa al'umma yin hijira zuwa garin Tambuwal, kuma hakan ya sa mutane da dama yin bore don nuna rashin jin daɗi kan tabarbarewar tsaro. A cikin wata sanarwa da mai taima...