Dan’iya ya nuna damuwa tare da goyon bayan kalaman Amnesty International kan karuwar ta’addanci a jihar Sokoto
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a Jihar Sokoto, Hon. Manir Muhammad Dan’iya, ya bayyana damuwa matuƙa kan ƙara yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a fadin jihar, inda ya goyi bayan kiran da Ƙungiyar Ƙare Haƙƙin Ɗan adam ta Amnesty International ta yi na gaggauta ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Dan’iya ya ce, "rahotannin da ke nuna yadda al’ummomi ke faɗawa cikin tashin hankali har ta kai suna barin garuruwansu da 'yan bindiga ke ƙonewa, tare da yin garkuwa da mata da ‘yan mata, sun nuna cewa matsalar tsaro ta kai matakin mai matuƙar muni da ke buƙatar haɗin gwiwar gwamnatin jihar da ta tarayya domin magance ta.
Ya bayar da misalin yadda 'yan bindiga suka afkawa mazauna ƙauyuka da dama da suka haɗa da Girkau da Romon Liman da Romon Sarki da Margai abin da ya tilasta wa al'umma yin hijira zuwa garin Tambuwal, kuma hakan ya sa mutane da dama yin bore don nuna rashin jin daɗi kan tabarbarewar tsaro.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkar yaɗa labarai, Aminu Abdullahi, ya sanya wa hannu, Dan’iya ya ce wajibi ne a ɗauki kiran da Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan adam ya Amnesty International a matsayin da muhimmanci kan halin da al’ummomin Sokoto ke ciki ba wai a ɗauke shi a matsayin kalaman siyasa ba. Ya ce zanga-zangar da aka yi a Tambuwal, ciki har da toshe hanyoyin mota daga Tambuwal zuwa Jega da Tambuwal zuwa Aleiro ta jihar Kebbi, na nuna takaicin jama’a da ke jin an yi watsi da su daidai lokacin da suke fuskantar tsananin hare-hare daga 'yan fashin daji.
Dan’iya ya nuna matuƙar damuwa har zuciyarsa tare zargi gwamnatin APC ta jihar Sokoto da rashin nuna kulawar gaggawa wajen fuskantar matsalar, inda ya ce shiru da gwamnati ke yi duk lokacin da hare-hare suka faru ya zama abin damuwa.
Ya bukaci hukumomin tsaro su ƙara kaimi wajen gudanar da ayyukan leƙen asiri da kuma tabbatar da kama da hukunta duk wanda aka.samu da laifin aikata ta'addanci.
Ɗan takarar ADC ya kuma tambayi yadda gwamnati ke tafiyar da dukiyar jama’a, inda ya ce matsalar tsaro ta sa buƙatar bayyana yadda ake kashe kuɗi ta zama dole. Ya yi nuni da cewa gwamnatin jihar da kananan hukumomi sun karɓi fiye da naira tiriliyan 1.2 daga Asusun Tarayya inda ya ce abin a bincika ne, ya kuma kalubalanci gwamnati ta bayyana a fili adadin kuɗin da aka ware domin samar da tsaro da ayyukan da suka shafi tallafin jin kai da kuma mayar da al’ummomin da abin ya shafa zuwa garuruwansu.
Ya ce matsalar tsaro ta taka rawa wajen ruguza tattalin arziki a jihar Sokoto, domin ta haddasa dubban manoma sun bar gonakinsu sannan rayuwar jama’a ta tabarbare, ilimi da tattalin arzikin ƙananan al’ummomi sun shiga wani hali na koma baya kuma maras tabbas. Don haka ya bukaci gwamnatin jihar ta samar da wani tsarin gaggawa na tallafawa ‘yan gudun hijira da taimaka wa iyalai da abin ya shafa tare da yin aiki da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya da zai taimaka wajen maido da martabar noma da kuma kasuwanci. Haka kuma ya bukaci gwamnatin tarayya ta ƙarfafa ayyukan tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Dan’iya ya yaba wa Amnesty International da sauran ƙungiyoyin da ke bayyana damuwa kan halin da jama’a ke ciki, tare da kira ga gwamnatin Sokoto ta daina tsuje bakinta kan abubuwan da suka zama wajibi a dauki mataki kan su. Ya jaddada cewa nauyin gwamnati shi ne kare rayukan jama’a ba tare da la’akari da siyasa da ma inda suka fito ko matsayi ba. “Babu wani dalili jihar Sokoto ba za ta ci gaba da rasa jama’arta ba yayin da shugabanni da aka ɗora wa nauyin kare su ke ci gaba da jan bakinsu su yi shiru ba. Jama’a na da hakkin samun cikakken tsaro kuma dole ne gwamnati ta dauki kowane rai a matsayin mai muhimmanci,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa idan ADC ta karɓi mulki, tsaro da kariyar al’umma da samar tallafin jin kai da kuma sarrafa dukiyar jama’a cikin gaskiya za su kasance ginshiƙan manufofinta. Ya kuma bukaci jama’a su tashi tsaye domin kare martabar kuri'ars a shekarar 2027.
Tantabara News jarida ce ta online mai tarin mabiya, da ke bayar da labarai ba tare da ɓoye gaskiya ba. Ku yi sharing da follow domin samun muhimman labaran siyasa da tarihi da nishadantarwa.
Comments