Skip to main content

Posts

Showing posts from February 5, 2023

Canjin Kuɗi Alfanu Ne - Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi, ya shawarcin 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi na canjin fasalin kuɗi, in da ya ce yana da muhimmanci. Ya roƙi 'yan Najeriya da su marawa tsarin baya, wanda a cewar sa  ba Najeriya ce ta farko a canza fasalin kuɗi ba a duniya, sai dai wannan ya zo da wahala ga jama'a amma kuma yana da matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasa  da walwalar jama'a duk da akwai buƙatar a inganta shi. Mista Obi ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a ƙarshen makon nan. Peter Obi dai ya taɓa zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a 2019 kafin yanzu shi ma ya fito neman wannan kujera a babban zaɓe mai zuwa.

INEC Ta Yaba Yadda Na'urar BVAS Ke Aiki

Shugaban Hukumar Zaɓe INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa gwajin da aka yi na tantance masu jefa kuri'a ya nuna na'urar BVAS da aka fito da ita na yin aiki yadda ya dace. Shugaban hukumar ya bayyana hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Tarayya Abuja. Ya ce "naurar na iya tantance masu zaɓe cikin dakika 30 kuma babu wata alamar tasgaro a tattare da ita". Farfesa Yakubu ya ce sun tanadi na'urorin wucin gadi ko da aka yi wasu daga cikin na'urorin su kasa lokacin da ake tantance mazu jefa kuri'a da su.