Skip to main content

Canjin Kuɗi Alfanu Ne - Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour Party Mista Peter Obi, ya shawarcin 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da shi na canjin fasalin kuɗi, in da ya ce yana da muhimmanci.
Ya roƙi 'yan Najeriya da su marawa tsarin baya, wanda a cewar sa  ba Najeriya ce ta farko a canza fasalin kuɗi ba a duniya, sai dai wannan ya zo da wahala ga jama'a amma kuma yana da matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasa  da walwalar jama'a duk da akwai buƙatar a inganta shi.
Mista Obi ya bayyana hakan a shafinsa na twitter a ƙarshen makon nan.

Peter Obi dai ya taɓa zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar a 2019 kafin yanzu shi ma ya fito neman wannan kujera a babban zaɓe mai zuwa.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey