Daga Zubairu Ahmad Bashir Gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya mika kokon baransa ga Hukuma Shirya Jarrabawar Share Fagen Shiga Jami'a (JAMB) da ta duna rokonsa kada ta ragewa daliban da ke son shiga jami'a makin da ake bukata kafin samun gurbi. Gwamnan ya shaidawa gidan talabijin na Channels haka ne a wata hira da aka yi da shi. Ya ce ko kusa ba taimakawa daliban hakan zai yi ba face mayar da su cima-kwance. El-Rufa'i ya kara da cewa yankin arewacin Najeriya na cikin halin koma baya a bangaren ilmi kuma tuni aka yi masa zarra a wannan fanni. A cikin hirar ya roki hukumar ta JAMB Allah-Ma'aiki da kada ta sassautawa kowane dalibi. Abu mafi kyau in ji shi shine su ci jarrabawar da za ta ba su makin da za su iya samun gurbin karatu a jami'o'i da manyan kwalejojin Najeriya. Idan ana iya tunawa dai an samu mummunar faduwar jarrabawar share fagen shiga jami'a ta bana, in da galibin wadanda suka zana ta suka kasa samun adadin m...