Skip to main content

Posts

Showing posts from February 20, 2021

Alamu Na Nuna Gwamna Wike Zai Shiga APC

Bayanai da ke fitowa yanzu haka na bayyana alamun gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike na daf da tsunduma jam'iyar APC mai mulki. An jiyo babban mai tsawatawa na majalisar wakilai ta tarayya Orji Uzo Kalu na bayar da tabbacin cewa tattaunawa ta yi nisa tsakaninsa da gwamna Wike. Kalu ya sanar da manema labaru a ranar alhamis cewa, bayan da gwamnan ya gayyace shi rangadin wasu ayukka da ke gudana a babban birnin jahar Fatakwal, ne suka tattauna kan wannan batun. Orji Kalu ya kuma ce sun shafe daren ranar suna shawarwari da gwamnan akan yadda zai shigo kana ya karfafa masa guiwa kan shiga jam'iyar APC, domin jawowa jahar ta Rivers alhairai masu yawa daga gwamnatin tarayya, in da kuma ya nuna yayi na'am da wannan shawara.