Skip to main content

Alamu Na Nuna Gwamna Wike Zai Shiga APC

Bayanai da ke fitowa yanzu haka na bayyana alamun gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike na daf da tsunduma jam'iyar APC mai mulki. An jiyo babban mai tsawatawa na majalisar wakilai ta tarayya Orji Uzo Kalu na bayar da tabbacin cewa tattaunawa ta yi nisa tsakaninsa da gwamna Wike. Kalu ya sanar da manema labaru a ranar alhamis cewa, bayan da gwamnan ya gayyace shi rangadin wasu ayukka da ke gudana a babban birnin jahar Fatakwal, ne suka tattauna kan wannan batun.
Orji Kalu ya kuma ce sun shafe daren ranar suna shawarwari da gwamnan akan yadda zai shigo kana ya karfafa masa guiwa kan shiga jam'iyar APC, domin jawowa jahar ta Rivers alhairai masu yawa daga gwamnatin tarayya, in da kuma ya nuna yayi na'am da wannan shawara.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.