Rahotanin da ke shigowa yanzu haka na cewa an samu rabuwar kai tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar PDP a jahar Bauchi in da jam’iyar ke shirin sake zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jahar. Wannan ya biyo bayan matakin da Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya dauka ne, da ya kekasa kasa ya ce ba zai bai wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya fadi zaben neman takarar shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi ba. Jaridar Daily Trust da DW Hausa duka sun ruwaito wannan labari.