Skip to main content

Posts

Showing posts from January 27, 2021

'Yan Bindiga Sun Sako Hakimin Radda Alhaji kabir Umar

Rahotannin da ke shigowa yanzu haka, na cewa maharan da suka sace hakimin Radda, Alhaji Kabir Umar sun sako shi. Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da sakin nasa, sai dai ba ta yi cikakken bayanin yarjejeniyar da aka cimma kafin sakin sa ba. A ranar 22 ga wannan watan na Janairun makon jiya dai ne maharan suka sace ce shi daga Katsina zuwa dajin Zamfara. 'Yan bindigar sun sako shi a daren jiya bayan kwana hudu da sace shi. Rahotanni sun ce jami'an gwamnatun jahar Katsina da hadin guiwa da jami'an tsaro sun samu tattaunawa da maharan, abinda ya kai ga sakinsa, sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa kafin sakin na sa ba.

Sabuwar Kwayar Korona Ta Bulla A Najeriya

A halin yanzu da duniya ke tsakiyar fargaba da rashin sanin makoma, Hukumar Yaki Da Cuta Mai Yaduwa ta NCDC da ke Najeriya, ta fitar da sanarwar barkewar sabon nau'in cutar annobar korona da aka lakabawa suna B.1.1.7. Wannan sabuwar kwayar cutar dai ta fi ta farko saurin yaduwa da matukar hadari wajen kashe mutane, da aka tabbatar da ta kan yadu da kashi 70 cikin dari fiye da na farkon. A watan Disamban 2020 aka samu rahoton bullar sabuwar koronar a kasar Burtaniya da Afirka ta Kudu. Shugaban hukumar NCDC ta kasa Chikwe Ihekweazu ya sanar da hakan a jiya. Ya bayyana cewa hukumar za ta kara azama don yin kandagarkin bazuwar sabon nau'in korona na B.1.1.7 tsakanin jama'a. Wani kwararren likitan Firaministan Burtaniya Boris Johnson mai suna Patrick Vallance, ya bayyana cewa, "daga marasa lafiya 'yan tsakanin shekaru 60 zuwa sama da suka harbu da tsohuwar kwayar cutar a kasar, 10 kan rasa rayukansu a cikin mutum 1000 kowace rana, amma a wannan karon, da wan...