Skip to main content

Posts

Showing posts from November 20, 2020

Ba Zamu Bar Korona Ta Haifar Muna Da Bashin Da Zai Ruguza Mu Ba - Antonio Gutarres

 A yau jumu'a sakataren Majalisar Dunkin Duniya, Antonio Gutarres ya bayyana cewa dimbin bashin da annobar korona ta jefa duniya ya wuce misali, baya ga yunwa da tashin hankali da sauran matsaloli da ke addabar kasashe musamman masu tasowa. Yana wadannan kalamai ne daidai lokacin da a karshen makon nan ake shirin gudanar da taron kolin kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki na duniya da aka fi sani da G-20.  Ya ce bai kamata bashi ya zama tarnaki ga ci gaban duniya ba. Ana ganin yana wannan magana ne da manufar tursasa manyan kasashe masu arziki da su yi sassauci ga matalautan kasashe a bangaren da ya shafi dimbin bashin da ake bin su. Gutarres ya ce, "kasashe masu arziki kamar Amurka da China ya dace su samar da sassauci da daidaito ga kasashe masu tasowa, domin taimaka mu su farfadowa". Ya yi nuni da irin illar da kin hakan za ta iya haifarwa duniya nan gaba, "kusan hanyar samar da kandagarkin Covid-19 ba ta wuce ta kudi ba, kenan bai dace a ce duk rana ta All...

Saudiyya Ta Harbo Jirgin Saman 'Yan Tawayen Houthi

 Kasar Saudiyya ta yi nasarar harbo wani jirgi maras matuki da aka gano na mayaka 'yan tawayen Houthi ne da ke Yamen. Kasar ta Saudiyya dai ta ce tuni mayakan 'yan tawayen da suka dade suna gwabza fada da gwamnatin Yamen da Saudiyyar ke marawa baya, suka sha alwashin kai ma ta hari. Jirgin maras matuki ya durfafi Saudiyya ne kafin daga bisani gungun kawancen da take dafawa yayi nasarar harbo shi.

Biden Ya Doke Trump A Georgia Da Ratar Kuri'u 12,284

 An kammala kirga kuri'un jahar Georgia da ake takaddama kan ta, in da Joe Biden ya lashe jahar da rata mai yawa. Jahar Atlanta Georgia mai yawan kuri'u miliyan biyar da doriya ta zama sha kallo a idon duniya ganin yadda shugaba Donald Trump ya yi zargin shi ne ya samu nasara a jahar kuma ya nemi sai an sake kirga dukan kurin'un da aka kada. A jiya alhamis da yamma ne aka kammala lissafin da ya kwashe kusan fiye da mako daya a na yi, in da ofishin sakataren gwamnatin jahar ya fitar da wannan sanarwa. Ofishin Brad Raffensperger ya bayyana cewa bayan sake kirga dukan kuri'un da hannu, sakamakon da aka samu tun farko yana nan bai sauya ba. Joe Biden ya doke Donald Trump da yawan kuri'u 12,284, yayin da shugaba Donald Trump ya samu 1,872.

Mai Tsaron Lafiyar Kakakin Majalisar Wakilai Ta kasa Ya Harbe Mai Sayar Da Jarida

 A jiya da yammaci ne dai lamarin ya faru in da daya daga jami'an da ke kare lafiyar kakakin majalisar wakilai na kasa, Femi Gbajabiamila ya yayi harbin da yayi sanadiyyar mutuwar wani mai tallar jarida. Gbajabiamila ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa, yana kan hanyar dawowa ya tsaya wajen don gaisawa da mutane, to sai wasu gungun mutane suka taso masa abinda ya sa masu tsaron lafiyarsa suka yi harbi, wanda ta kai ga samun daya daga cikin masu sayar da jaridun da ke wurin. Bayanan da TANTABARA ta samu na cewa an dakatar da jami'n da ake zargi da yin harbin, har sai an kammala bincike. Galibin lokuta ana zargin jami'an tsaron Najeriya da yin harbin da kan jawo hallakar mutane, wanda ko kwanan baya irin haka ta faru a Kano in da ake zargin jami'an tsaron 'yan sanda da hallaka wasu mutane uku bisa harbin da ake zargin na kuskure ne.