Kasar Saudiyya ta yi nasarar harbo wani jirgi maras matuki da aka gano na mayaka 'yan tawayen Houthi ne da ke Yamen.
Kasar ta Saudiyya dai ta ce tuni mayakan 'yan tawayen da suka dade suna gwabza fada da gwamnatin Yamen da Saudiyyar ke marawa baya, suka sha alwashin kai ma ta hari.
Jirgin maras matuki ya durfafi Saudiyya ne kafin daga bisani gungun kawancen da take dafawa yayi nasarar harbo shi.
Comments