A yau jumu'a sakataren Majalisar Dunkin Duniya, Antonio Gutarres ya bayyana cewa dimbin bashin da annobar korona ta jefa duniya ya wuce misali, baya ga yunwa da tashin hankali da sauran matsaloli da ke addabar kasashe musamman masu tasowa.
Yana wadannan kalamai ne daidai lokacin da a karshen makon nan ake shirin gudanar da taron kolin kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki na duniya da aka fi sani da G-20.
Ya ce bai kamata bashi ya zama tarnaki ga ci gaban duniya ba. Ana ganin yana wannan magana ne da manufar tursasa manyan kasashe masu arziki da su yi sassauci ga matalautan kasashe a bangaren da ya shafi dimbin bashin da ake bin su.
Gutarres ya ce, "kasashe masu arziki kamar Amurka da China ya dace su samar da sassauci da daidaito ga kasashe masu tasowa, domin taimaka mu su farfadowa".
Ya yi nuni da irin illar da kin hakan za ta iya haifarwa duniya nan gaba, "kusan hanyar samar da kandagarkin Covid-19 ba ta wuce ta kudi ba, kenan bai dace a ce duk rana ta Allah muna dora bashin biliyoyin kudaden a wuyan al'umma mai tasowa ba", in ji Gutarres.
Comments