Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana bukatar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a karo na biyar, in da ya ce ya wajaba ne ya karba kiran jama'a. Atiku ya yi wannan magana ne a birnin tarayya Abuja lokacin da ya ke sanar da muradin nasa, "Abubuwan da suka ja hankalina na da yawa, muhimmai daga cikin su akwai bukatar samar da hadin kai, tsaro da tattalin arziki, ciyar da bangarorin gwamnatin tarayya gaba da sauran su". Atiku Abubakar na bayyana wannan ne daidai lokacin da gwamnan jahar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya bayyana anniyarsa ta tsayawa neman shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar ta PDP. Tambuwal ya ce babu wani da ya fi dacewa ya mulki kasar nan a wannan lokaci da ake ciki idan ba shi ba. Ya bayyana kan sa a matsayin matashi kuma wanda ya goge a harkar siyasa masanin dubarun mulki da ya san makomar Najeriya...