Skip to main content

An Tilas Ni Tsayawa Takara - In Ji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana bukatar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a karo na biyar, in da ya ce ya wajaba ne ya karba kiran jama'a.
Atiku ya yi wannan magana ne a birnin tarayya Abuja lokacin da ya ke sanar da muradin nasa, "Abubuwan da suka ja hankalina na da yawa, muhimmai daga cikin su akwai bukatar samar da hadin kai, tsaro da tattalin arziki, ciyar da bangarorin gwamnatin tarayya gaba da sauran su".
Atiku Abubakar na bayyana wannan ne daidai lokacin da gwamnan jahar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya bayyana anniyarsa ta tsayawa neman shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar ta PDP.
Tambuwal ya ce babu wani da ya fi dacewa ya mulki kasar nan a wannan lokaci da ake ciki idan ba shi ba. Ya bayyana kan sa a matsayin matashi kuma wanda ya goge a harkar siyasa masanin dubarun mulki da ya san makomar Najeriya.
Da dama daga 'yan Najeriya na ganin jam'iyyar za ta fuskanci babbar barazana ganin masu neman tsayawa takara karkashinta fitattu ne, da suka hada da tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya yi maraba da irin yadda magoya bayansa ke bayyana shi da mafi dacewa ya mulki kasar nan. An bayyana Kwankwaso a matsayin gogaggen dan siyasa da ya sha nuna burin tsayawa takarar kujerar shugaban Najeriya. Ganin ya fito a jaha mafi yawan jama'a a Najeriya kuma wadda duk mai son samun nasara a zabe ya zama wajibi ya taka muhimmiyar rawa wajen samun kuri'u a Kano ya sa wasu ke ganin za a samu kalubale gagarumi wajen tsayar da dan mutum daya da zai yi ma PDP takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Comments