Afirka nahiya ce mai dogon tarihi. Tun asali, yawancin Turawa sun yi kokarin sanya idanu a kan nahiyar, sun ziyarce ta don neman ko dai kasuwanci, wanda a wancan lokacin wani nau'i ne na cinikin bayi ko kuma daga baya ya koma ga cinikin kayan masarufi kamar su gyada, auduga, fatun dabbobi da makamantansu. Zuwan Larabawa kuma, a wasu lardunan Afirka na lokacin, gami da yankin da ake kira "Sudaniyya", wanda ya hada da Sudan, Najeriya, Chadi, da wasu sassan Jamhuriyar Nijar, ya haifar da yaduwar Musulunci da al'adun Gabas. Daga baya, zuwan Bature ya kawo kiristanci, ilimin yamma da sauran manufofin Turawa. Nahiyar Afirka sannu a hankali tana juyawa zuwa matakai daban-daban; daga duhun kai har zuwa halin da ake ciki a yau. Ilimin addini da na zamani sun samu gindin zama a kasashen Afirka, amma har yanzu mata suna baya a wannan tafiyar. Sau da yawa za ka ga mata a yankunan karkara har ma da wasu biranen Afirka ci...