Skip to main content

Farkawar Matan Afirka

Afirka nahiya ce mai dogon tarihi. Tun asali,  yawancin Turawa sun yi kokarin sanya idanu a kan nahiyar, sun ziyarce ta don neman ko dai kasuwanci, wanda a wancan lokacin wani nau'i ne na cinikin bayi ko kuma daga baya ya koma ga cinikin kayan masarufi kamar su gyada, auduga, fatun dabbobi da makamantansu.
Zuwan Larabawa kuma, a wasu lardunan Afirka na lokacin, gami da yankin da ake kira "Sudaniyya", wanda ya hada da Sudan, Najeriya, Chadi, da wasu sassan Jamhuriyar Nijar, ya haifar da yaduwar Musulunci da al'adun Gabas.Daga baya, zuwan Bature ya kawo kiristanci, ilimin yamma da sauran manufofin Turawa.Nahiyar Afirka sannu a hankali tana juyawa zuwa matakai daban-daban; daga duhun kai har zuwa halin da ake ciki a yau.Ilimin addini da na zamani sun samu gindin zama a kasashen Afirka, amma har yanzu mata suna baya a wannan tafiyar.
Sau da yawa za ka ga mata a yankunan karkara har ma da wasu biranen Afirka cikin yanayin talauci da jahilci ba tare da samun wadataccen ilimi ba.Kowace rana, ana ganin mata dauke da itacen girki, wasu dauke da jarirai a bayansu suna zuwa rafuka ko ma gonaki don noman abinci da za a ci.
A irin wannan tsari mai kama da bauta, akwai kabilu a arewacin Najeriya da kuma kudanci inda matansu ke noma, suna renon yara da kuma dafa abinci a gida.
Hasali ma dai, a kudancin Najeriya, akwai kabilun da ke hana mata gadon iyayensu da suka mutu.
Al'ada da ra'yi na waɗannan kabilun, maza ne kawai da haƙƙin gado har ma da matar mutumin, koda kuwa mamacin mahaifinsa ne.
Wannan halin ya samo asali ne sakamakon rashin ilimin zamani da na addini wanda yawancin mata suke dashi.
A kasashe irin naTurai da Amurka mata suna da 'yanci  da ya yi daidai da al'adunsu da addininsu, kenan abu ne mai kyau idan a Afirka mutane sun rike addininsu tare da kyawawan al'adunsu, kuma su guji nuna bambanci da hadama.
A cikin addini babu wani wuri da ake hana kowace mace gado, sai dai ga kowane addini akwai wani tsari na musamman kuma mabiyansa sun yi imani da shi, kuma ba za su yarda da shisshigi daga wasu ba.

Ba Afirka kawai ake samun irin wannan ba har ma a kasashen Larabawa da na Asiya, inda har yanzu ake tauye ‘yancin mata ta hanyar hana su damar samun ilimi, sana’o’in dogaro da kai har ma da 'yancin auren wanda suke so; maimakon haka, zabin magabatansu shine zabinsu ko suna so ko basa so.
Duk da haka, wannan É“angaren na matan Afirka a yanzu yana neman taimako ta hanyoyi da yawa, gami da goyon bayan magabatansu kamar iyaye da mazajensu da goyon bayan gwamnatoci har ma shugabannin addinai.

Comments