Skip to main content

Posts

Showing posts from March 17, 2022

Buhari Ya Ce Maimala Ne Shugaban APC

A wani abu da ake ganin kamar zai iya haddasa sabuwar baraka a cikin jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci gwamnonin APC su bar gwamnan jahar Yobe Maimala Buni ya dore kan shugabancin jam'iyyar. Gwamnan dai ya isa birnin Landan tare da rakiyar Ministan ilmi Malam Adamu Adamu, in da kuma ya gana da shugaban kasar. A farkon makon jiya dai ne wasu jiga-jigan jam'iyyar APC suka maye gurbinsa da gwamnan jahar Naija Abubakar Sani Bello, wanda nan take ya rantsar shugabannin kwamitin gudanane da babban zaben jam'iyyar na kasa da ane sa ran yi a ranar 26 ga wannan wata na Maris. An jiyo gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa'i a wata hira da tashar talabijin ta Channels na cewa, gwamnan jahar Naija ne ya samu sahakewar shugaban kasa. El-Rufa'i ya ce, sun kafa wani kwamiti da suka tuntubi shugaban kasar, in da kuma ya amince da Sani Bello a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar APC na kasa. A ganin masana, wasu na amfani da sunan shugaba...

Shugaban Rasha Ya Nunawa Biden Yatsa

ewn.co.za Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce kalaman da shugaban Amurka Joe Biden ya yi ba za su tafi a banza ba. Yana dai mayar da martani ne akan kalaman shugaba Amurka da ya ce, "Putin azzalumi ne kuma wanda ya aikata manyan laifukan yaki". Sai dai shugaba Putin ya ce ba za ta taba yuwa Rasha ta yafe ma Amurka ta kowane fanni ba sakamakon wadannan kalamai da ya kira, "na cin zarafin kasarsa". Yanzu haka dai yakin da kasashen Ukraine da Rasha ke ci gaba da gwabzawa ya shiga mako na uku in da munana hare-haren da dakarun Rasha ke kaiwa suka yi sanadiyyar hallakar fararen hula da dama, ciki kuwa har da yara kanana. npr.org Kasashen da ke karkashin kungiyar tsaro ta NATO sun zakuda gefe guda ba tare da amincewa su tsunduma cikin yakin ba, in da suka bayar da hujjar cewa tsunduma yakin na iya haifar da yakin duniya na uku. Sai dai a maimakon haka sun tsananta sakawa Rasha karin takunkumai da suka hada da kin sayen man da ta ke hakowa, da...