Skip to main content

Buhari Ya Ce Maimala Ne Shugaban APC

A wani abu da ake ganin kamar zai iya haddasa sabuwar baraka a cikin jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci gwamnonin APC su bar gwamnan jahar Yobe Maimala Buni ya dore kan shugabancin jam'iyyar.
Gwamnan dai ya isa birnin Landan tare da rakiyar Ministan ilmi Malam Adamu Adamu, in da kuma ya gana da shugaban kasar. A farkon makon jiya dai ne wasu jiga-jigan jam'iyyar APC suka maye gurbinsa da gwamnan jahar Naija Abubakar Sani Bello, wanda nan take ya rantsar shugabannin kwamitin gudanane da babban zaben jam'iyyar na kasa da ane sa ran yi a ranar 26 ga wannan wata na Maris.
An jiyo gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa'i a wata hira da tashar talabijin ta Channels na cewa, gwamnan jahar Naija ne ya samu sahakewar shugaban kasa.
El-Rufa'i ya ce, sun kafa wani kwamiti da suka tuntubi shugaban kasar, in da kuma ya amince da Sani Bello a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar APC na kasa.
A ganin masana, wasu na amfani da sunan shugaba Buhari wajen juya akalar gwamnati ko cimma wani buri na kashin kai, hanin yadda kowane bangare ke fitowa yana bayyana cewa Buhari ne ya goyi bayan bangarensa.
Wannan dai a cewar masu lura da al'amurran yau da kullum a Najeriya, ba zai haifar da kome ba face rabuwar kai, a daidai lokacin da babban zaben kasar ke karatowa.

Comments