ewn.co.za
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce kalaman da shugaban Amurka Joe Biden ya yi ba za su tafi a banza ba. Yana dai mayar da martani ne akan kalaman shugaba Amurka da ya ce, "Putin azzalumi ne kuma wanda ya aikata manyan laifukan yaki".
Sai dai shugaba Putin ya ce ba za ta taba yuwa Rasha ta yafe ma Amurka ta kowane fanni ba sakamakon wadannan kalamai da ya kira, "na cin zarafin kasarsa".
Yanzu haka dai yakin da kasashen Ukraine da Rasha ke ci gaba da gwabzawa ya shiga mako na uku in da munana hare-haren da dakarun Rasha ke kaiwa suka yi sanadiyyar hallakar fararen hula da dama, ciki kuwa har da yara kanana.
npr.org
Kasashen da ke karkashin kungiyar tsaro ta NATO sun zakuda gefe guda ba tare da amincewa su tsunduma cikin yakin ba, in da suka bayar da hujjar cewa tsunduma yakin na iya haifar da yakin duniya na uku. Sai dai a maimakon haka sun tsananta sakawa Rasha karin takunkumai da suka hada da kin sayen man da ta ke hakowa, da rufe asusun ajiyar manyan jami'ai da 'yan kasuwar kasar da sauran su.
Wace matsala wannan yakin ya jawo ma duniya?
Wannan mataki ya kara sa farashin mai da suaran kayan abinci hauhawa a duniya. Kasashen Amurka da Burtaniya sun mika kokon baransu ga wasu kasashe masu arzikin man fetur kamar Saudiyya da Burtnaiya ta nemi ta kara yawan man da ta ke hakowa a kwanan nan, sai kuma dangantakar Amurka da Venezuela da ta dade da yin tsami amma kuma Amurka na ta zawarcin gwamnatin kasar domin samun matsaya daya akan sayar mata da mai.
Yadda farashin abinci zai iya karuwa a duniya
Kasar Ukraine ce ta daya wajen samar da kashi 30 na alkamar duniya. Hakan ya sa farashin alkama ya kara tashi, wanda wannan na iya shafar kasashen dama.
Yanzu haka akwai kasashen da wannan ta soma shafuwar tattalin arzikinsu. Kwanan nan kasashen Afirka irin Masar da Nijar da Mali da Tunisiya da wasu kasashen Asiya kamar Malesiya da Indunisiya suka kara farashin buredi da sauran kayan da akan sarrafa da alkama kamar biskit da fankaso da fankeke da sauran su. A makon jiya ma sai da aka yi wata zanga-zanga a Sudan sakamakon farashin buredi da ya yi tashin gwauron zabo mai alaka da karancin alkama a duniya.
Haka ma kasar Aljeriya ta bayar da sanarwar dakatar da sayar da sukari da nau'in kayan abinci ga sauran kasashe makwabta a dalilin tsadar kayan sarrafa su da kuma karancin su da duniya ke fuskanta sakamakon wannan yaki.
Comments