Skip to main content

Posts

Showing posts from February 9, 2023

Filin Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Zai Ci Naira Biliyan 700

Ministan suhurin jiragen sama Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa majalisar zartaswata ƙasa ta amince da ware fiye da naira biliyan ɗari bakwai domin aikin kwangilar gyaran filin sauka da tashin jiragen na sama na duniya na Malam Aminu Kano, wanda ya ce za kammala a cikin shekara ɗaya rak. Majalisar zartaswa ta ƙasa ta kuma amince da ware naira biliyan ɗari da goma sha bakwai domin gudanar da kwangilar gina cibiyar bincike akan man fetur ta Oloibir a yankin Naija Delta. Ministan ƙasa a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya shaidawa ‘yan jaridar fadar shugaban ƙasa hakan, inda ya ce za a kammala aikin kwangilar a cikin shekaru biyu da rabi. Ya ce tun a 1980 gwamnatin Alhaji Shehu Aliyu Shagari ta soma aikin, amma daga bisani aka yi watsi da shi wanda a yanzu zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za a ci ga da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Kotu Ta Tabbatar Da Peter Obi Matsayin Ɗan Takarar Jam'iyyar LP

Kotun ɗaukaka ƙara mai mazuninta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APM ta shigar inda take neman a hanawa Peter Obi na jam’iyyar Labour damar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa. Waɗanda ake ƙarar su ne Hukumar Zaɓe mai zaman kanta, INEC da jam’iyyar Labour da kuma ɗan takararta Mista Peter Obi. Da ta ke yanke hukuncin tare da taimakon alƙalai uku, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta amince da yin watsi da shari’ar a dalilin rashin cikakkun hujjoji. Alaƙalan kotun sun nemi masu saka ƙarar da su biya waɗanda ake ƙara tarar naira dubu ɗari biyu a dalilin ɓata mu su lokaci.