Kotun ɗaukaka ƙara mai mazuninta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APM ta shigar inda take neman a hanawa Peter Obi na jam’iyyar Labour damar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa.
Waɗanda ake ƙarar su ne Hukumar Zaɓe mai zaman kanta, INEC da jam’iyyar Labour da kuma ɗan takararta Mista Peter Obi.
Da ta ke yanke hukuncin tare da taimakon alƙalai uku, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta amince da yin watsi da shari’ar a dalilin rashin cikakkun hujjoji.
Alaƙalan kotun sun nemi masu saka ƙarar da su biya waɗanda ake ƙara tarar naira dubu ɗari biyu a dalilin ɓata mu su lokaci.
Comments