Skip to main content

Hukumar Hana Fasa Kwabri Ta Najeriya Ta Kama Buhunan Naman Jaki 1,339

Hukumar ta bayyana kama wannan adadin buhunan naman jaki ne a jahar Kabi da ke arewa maso yammacin Najeriya da aka kiyasta kudinsu ya haura naira miliyan 40.
Shuguban hukumar ta kastam Joseph Attah ya ce sun yi nasarar kama kyafaffen naman jakin ne da aka shirya fita da shi. A cewar sa wadanda aka kama da naman sun bayyanawa hukumar cewa fiye da jakuna dubu daya suka yanka kafin su tara wannan adadi.

Gwamnatin Najeriya dai ta haramta safarar jakuna zuwa kasashen ketare musamman kasar Sin, wadda ke sahun gaba wajen sayen jakuna a kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Nijar da Mali da Sudan da sauran su.

A halin da ake ciki yanzu haka jakuna na barazanar karewa a duniya sakamakon yawan safarar su da ake tare da sarrafa nama da fatarsu ta wasu hanyoyi na daban.
Hasalima dai, jaki dabba ce da kan hai fi da daya kwal a cikin shekaru ba kamar sauran dabbobi ba da ke haihuwa biyu zuwa uku a shekara.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey