Skip to main content

Posts

Showing posts from May, 2022

PDP Na Son Sake Zaben Fidda Gwani A Jahar Bauchi

Rahotanin da ke shigowa yanzu haka na cewa an samu rabuwar kai tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar PDP a jahar Bauchi in da jam’iyar ke shirin sake zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jahar. Wannan ya biyo bayan matakin da  Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya dauka ne, da ya kekasa kasa ya ce ba zai bai wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya fadi zaben neman takarar shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi ba. Jaridar Daily Trust da DW Hausa duka sun ruwaito wannan labari.

Abubakar Gada Da Salame Sun Janye Daga Zaben Fidda Gwanin APC A Sokoto

Sanata Abubakar Gada da Abdullahi Balarabe Salame sun fitar da sanarwar janyewa daga zaben fitar da gwani na gwamna a jahar Sokoto bayan wata takaddama da ta biyo baya. Takardar da suka fitar ta bayyana cewa tun farko sun nemi a yi zaben ta hanyar 'yar tinke, amma kuma wani bangare na jam'iyyar ya yi watsi da wannan. Sun ce ganin ba za a yi mu su adalci ba ya sa ba za su shiga zaben ba, kuma suna kira ga uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta duba yuwar bin bukatar da suka nema tun da farko. A cewar takardar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa duk zaben da aka yi ba tare da amfani da masu zaben 'yan takara da aka fi sani da delegate, ko kuma ta hanyar sulhuntawa ba to haramtacce ne. Kan haka suke neman uwar jam'iyyar da ta san dacewa ba a yi zabe a jahar Sokoto ba, kuma wannan zai iya jawo jam'iyyar APC ta rasa dan takara, in ji su.

Zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto A Jam'iyyar PDP Ya Bar Baya Da Kura

Bayan da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci zaman sulhu domin tsayar da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP tare da zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma, hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin jama'a. Daga cikin jerin 'yan takarar da suka nemi kujerar akwai mataimakin gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Maniru Muhammed Daniya da kwamishin muhalli na jahar Sokoto, Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa da tsohon sakataren gwamnatin jahar Sokoto, Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma da kuma tsohon mataimakin gwamnan jahar Sokoto Alhaji Muktari Shagari. Bayan zama da gwaman Aminu Waziri Tambuwal ya yi da dukan su a dakin taro na kasa da kasa da ke Kasarawa, daga karshe gwamnan ya tabbatar da Sa'idu Umar Ubandoma a matsayin wanda zai yi ma jam'iyyar PDP takarar gwamna a 2023. Rahotannin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da cewa shi ma daya daga 'yan takarar da bai yi nasara ba, Alhaji Muntari Shagari ya fice daga jam'iyar ta PDP sai d

Gwamnatin Jahar Sokoto Ta Sanya Dokar Hana Yawo Tsawon Sa'a 24

Gwamnatin jahar Sokoto ta bayar da sanarwar saka dokar hana yawo a birnin Sokoto da wasu sassan jahar na tsawon sa'a 24. Ofishin mai ba gwamna shawara akan lamurran watsa labarai ne ya fitar da wannan sanarwa ranar asabar 14/05/2022. A cewar sanarwar, an dauki matakin ne don samar da zaman lafiya a jahar. Wannan nan dai na zuwa ne lokacin wata sabuwar zanga-zanga ta barke a birnin na Sokoto, wanda ke da nasaba da kamen da 'yan sanda suka yi na mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Debirah Samuel Yakubu a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari kwana biyu da suka gabata. In da da farko zanga-zangar da aka soma ta lumana ta rikide zuwa kone-kone. In da masu zanga-zangar suka cika harabar Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III.

An Kashe Wata Daliba Da Aka Zarga Da Batanci Ga Manzon Allah A Jahar Sokoto

Wata dalibar Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, mai suna Debora Samuel, ta gamu da ajalinta lokacin da wasu matasa da ba a kai ga sanin ko su wanene ba suka kashe ta hanyar kona ta, bayan da aka zarge ta da yin batanci ga Annabi mai tsira da amincin Allah. Lamarin ya kazance ne bayan da wasu daga daliban kwalejin suka yi zargin cewa ta dade ta na wannan batancin abinda ya kai ga barkewar rikicin da ya kai ga salwantar ranta. Tuni dai mahukuntan jahar Sokoto suka bayar da sanarwar rufe kwalejin har a kammala bincike. Babban sakatare a ma'aikatar ilmi mai zurfi ta jahar Sokoto Alhaji Almustapha Usman Ali, ya shaidawa manema labarai cewa, an bayar da umurnin rufe kwalejin kazalika za su sanar da jama'a mataki na gaba idan har an kammala bincike. An dai girke jami'an tsaro a harabar makarantar domin dakile rikicin da ka iya tasowa. Tuni dai da hotunan bidiyo da Tantabara ba ta kai ga tantantace sahihancinsu ba, suka karade shafukan sada zumunta, wadanda k

Daliban Jahar Sokoto Ba Zasu Rubuta Jarabawar WAEC Ba

Hukumar Shirya Jarabawar Sakandire ta Afirka ta Yamma wato WAEC, ta bayyana cewa jahohin Sokoto da Zamfara ba su aike mata da sunayen dalibansu da za su rubuta jarabbawar kammala babbar sakandire ba, wadda za a soma tsakanin ranakun 16 zuwa 23 ga watan Yunin gobe, kamar yadda sakataren hukumar shirya jarabawar Mista Patrick Aregan ya fitar da sanarwa. Sai dai a hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kwamishinan ilmi na jahar Sokoto Bello Abubakar Guiwa, ya ce matsalar ba daga gare su ba ne.  Kwamishinan ya ce hukumar ta WAEC ta fito ne da wani tsari na sun amsar kudi ba gaira ba dalili gare su wanda ya sa suka yi watsi da ita. Ya kara da cewa suna da dalibai kusan 30,000 da zasu rubuta jarabawa a wannan shekara, to amma sai hukumar hana su lambobin jarabawar da ake rabawa dalibai ta kuma ce duk wani kuskure daya da aka samu akan kowane dalibi, wajibi ne sai an biya naira 5000, wanda kuma miliyoyin kudade ne, kazalika sai gwamnatin jahar Sokoto ta biya kashi 40 cikin dari kafin som

ASUU Ta Tsunduma Sabon Yajin Aikin Watanni Uku

Kungiyar Malaman Jami'a ASUU ta fitar da wata sabuwar sanarwa a yau litinini 09/05/2022 da ta bayyana sake tsunduma wani sabon yajin aikin makonni 12. ASUU ta bayyana rashin gamsuwa da yadda bangaren gwamnatin tarayya ya dauki lamarin ba tare da muhimmanci ba. Sanarwar ta ASUU ta kuma nunar da yadda gwamnatin tarayya ta sa kafa ta shure yarjejeniyar da suka yi a 2020, tare da cewa babu wata alamar gwamnati da gaske ta ke. Kungiyar Malaman Jami'ar dai ta kwashe wata hudu tana yajin aiki kafin sake saka wani sabon wa'adi a yau na tsawon makonni 12 abinda masana harkar ilmi ke cewa ya gurgunta sha'anin ilmi a Najeriya.

Zan Yi Amfani Da Kundin Tsarin Mulki Ba Alkur'ani Ba - Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jahar Zamfara sanata Sani Yariman Bakura ya ayyana manufarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar APC. A wata hira da BBC Hausa Yariman Bakura ya bayyana cewa Najeriya na fama da matsaloli uku da zai mayarwa hankali idan aka zabe shi, da suka hada da tsaro da jahilci da talauci. Da aka tambai shi ko bai ganin wadanda ba musulmi ba na iya dari dari a zabensa. Sai ya ce a yanzu kam sabanin wancan lokaci da aka sani da kundin tsarin mulki zai yi amfani wajen rantsuwar kare Najeriya. Ya kuma kara da cewa a lokacin kaddamar da manufar tsayawarsa takara akwai limaman kiristoci daga Zamfara da wasu wurare a Najeriya da suka halarta, wanda alama ce da ke nuna zai yi ma kowa adalci a cewar sa. Sanata Sani Yariman Bakura dai shi ne gwamna na farko da ya assasa shari'ar Musulunci a jahar Zamfara a shekarar 2000. Wanda daga baya aka samu jahohin Sokoto da Kano suka bi sahu.  Abinda ya jawo karo na farko a tarihi gwamnatin jahar Zamfara ta