Sanata Abubakar Gada da Abdullahi Balarabe Salame sun fitar da sanarwar janyewa daga zaben fitar da gwani na gwamna a jahar Sokoto bayan wata takaddama da ta biyo baya.
Takardar da suka fitar ta bayyana cewa tun farko sun nemi a yi zaben ta hanyar 'yar tinke, amma kuma wani bangare na jam'iyyar ya yi watsi da wannan. Sun ce ganin ba za a yi mu su adalci ba ya sa ba za su shiga zaben ba, kuma suna kira ga uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta duba yuwar bin bukatar da suka nema tun da farko.
A cewar takardar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa duk zaben da aka yi ba tare da amfani da masu zaben 'yan takara da aka fi sani da delegate, ko kuma ta hanyar sulhuntawa ba to haramtacce ne. Kan haka suke neman uwar jam'iyyar da ta san dacewa ba a yi zabe a jahar Sokoto ba, kuma wannan zai iya jawo jam'iyyar APC ta rasa dan takara, in ji su.
Comments