Skip to main content

Posts

Showing posts from March 4, 2021

Ba Za Kara Sace Kowa Ba A Najeriya - Inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen ci gaba da satar jama'a a fadin Najeriya. An dai jiyo hakan ne a ta bakin Ministan sufurin jiragen sama na kasa, Sanata Hadi Sirika lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin tarayya don yiwa gwamnatin jahar Zamfara jaje, akan daliban Makarantar Kimiyya ta 'Yan Mata ta Jangebe su kimanin 300 da aka sace. Sirika ya ce wannan shi ne na karshe, domin kuwa gwamnatin tarayya za ta dauki sabbin matakai da za su taimaka wajen dakushe ayukkan ta'addanci da suka mamaye yankunan arewa. Ya kara da cewa Buhari ya nuna damuwarsa matuna kan yadda ayukkan ta'addanci ke dada raruwa. Shugaban kasar ya kuma yabawa gwamnan jahar Zamfara saboda kokarinsa wajen yaki da matsalar tsaro. Shi ma gwamnan jahar Zamfara, Bello Mutawalle ya bayyana jin dadi akan yadda gwanatin tarayya ke nuna kulawarta akan wannan lamari.

No More Abduction In Nigeria - Says Buhari

Nigerian President Muhammadu Buhari has assured Nigerians that abduction of 300 female students from Government Girls Science Secondary School, Jangebe, Zamfara State, would be the last to happen in the country. Minister of Aviation, Senator Hadi Sirika, conveyed Buhari’s declaration when he led a high-powered federal government delegation to sympathise with the people and government of Zamfara State. According to him, 'Buhari is assuring the citizens there would be no abduction again because the Federal Government would show its commitment in fighting banditry and other forms of insecurity in the country’.  The minister said new measures have been developed by the federal government which would bring complete end to all forms of criminality in the nation. Sirika said the president is agitated by the setback and increase of banditry in almost everywhere in the north, which he noted that would not be tolerated. Buhari also commends zamfara State Governor, Bello Matawalle