Skip to main content

Ba Za Kara Sace Kowa Ba A Najeriya - Inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen ci gaba da satar jama'a a fadin Najeriya.
An dai jiyo hakan ne a ta bakin Ministan sufurin jiragen sama na kasa, Sanata Hadi Sirika lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin tarayya don yiwa gwamnatin jahar Zamfara jaje, akan daliban Makarantar Kimiyya ta 'Yan Mata ta Jangebe su kimanin 300 da aka sace.
Sirika ya ce wannan shi ne na karshe, domin kuwa gwamnatin tarayya za ta dauki sabbin matakai da za su taimaka wajen dakushe ayukkan ta'addanci da suka mamaye yankunan arewa.
Ya kara da cewa Buhari ya nuna damuwarsa matuna kan yadda ayukkan ta'addanci ke dada raruwa.
Shugaban kasar ya kuma yabawa gwamnan jahar Zamfara saboda kokarinsa wajen yaki da matsalar tsaro.

Shi ma gwamnan jahar Zamfara, Bello Mutawalle ya bayyana jin dadi akan yadda gwanatin tarayya ke nuna kulawarta akan wannan lamari.

Comments