Gamayyar jam'iyyun adawa 13 sun bayyana cewa za su Ęauracewa shiga zaÉe muddin Babban Bankin Najeriya (CBN) ya Ęara wa'adin amfani da tsofaffin kuÉaÉe daga lokacin da aka Éiba tun da farko. Shugaban jam'iyyar AA Kennetth Udeze ne ya fitar da wannan sanarwa, in da ya ce canjin fasalin kuÉi da CBN ya fito da shi zai haifar da babban tasiri a tattalin arziki da fannin tsaro kana sun kai matsayar watsi da sabon matakin da gwamnonin APC suka Éauka da suka haÉa da na Kaduna, Malam Nasiru El-rufai da na Zamfara Bello Mutawalle da na Kogi Yahaya Bello, na maka shugaban Ęasa Muhammadu Buhari a gaban kotu kan sauya takardun kuÉi da ya yi. A Najeriya akwai jerin jam'iyyu 18 da za su fafata a babban zaÉe mai zuwa sai dai 13 daga ciki sun yi barazanar janye jikinsu daga shiga zaÉen muddin aka Ęara lokacin amfani da tsofaffin kuÉaÉe. Menene ra'ayinka kan wannan batu?