Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar masa da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar da magoya bayansa, na taƙama da cewa ba sa buƙatar goyon bayan gwamnonin G5 kafin su ci nasara zaɓe, saboda wasu tsiraru a fadar shugaban ƙasa sun ba su tabbacin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Jaridar POLITICS NIGERIA ta ruwaito cewa gwamnan yayi magana ne a garin Ibaka a yayin gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas na ƙaramar hukumar Okrika a ranar Juma’a.
"Na ce an ba su tabbaci, amma wannan zaɓen ba zai dogara ne akan wannan tabbacin ba, yana kan tabbacin mutane ne,” in ji Wike.
Gwamna Wike dai ya dage cewa har yanzu Atiku na buƙatar jihar Ribas don samun nasara ko kuma ya faɗi zaɓe a 2023.
A cewarsa, “ko kuna so ko ba ku so, dole ne ku buƙaci jihar Ribas. Idan ba ku buƙatar Jihar Ribas to dole ne ku sha ƙasa. Idan kun ce ba ku son mu, lallai kuwa za ku gaza kai bantenku". In ji Wike.
Comments