Skip to main content

Jam'iyyu 13 Sun Yi Barazanar Ƙauracewa Zaɓe A Najeriya

Gamayyar jam'iyyun adawa 13 sun bayyana cewa za su ƙauracewa shiga zaɓe muddin Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa'adin amfani da tsofaffin kuɗaɗe daga lokacin da aka ɗiba tun da farko.
Shugaban jam'iyyar AA Kennetth Udeze ne ya fitar da wannan sanarwa, in da ya ce canjin fasalin kuɗi da CBN ya fito da shi zai haifar da babban tasiri a tattalin arziki da fannin tsaro kana sun kai matsayar watsi da sabon matakin da gwamnonin APC suka ɗauka da suka haɗa da na Kaduna, Malam Nasiru El-rufai da na Zamfara Bello Mutawalle da na Kogi Yahaya Bello, na maka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gaban kotu kan sauya takardun kuɗi da ya yi.

A Najeriya akwai jerin jam'iyyu 18 da za su fafata a babban zaɓe mai zuwa sai dai 13 daga ciki sun yi barazanar janye jikinsu daga shiga zaɓen muddin aka ƙara lokacin amfani da tsofaffin kuɗaɗe.

Menene ra'ayinka kan wannan batu?

Comments