Skip to main content

Yadda Masu Kuɗi Da Ruwa Suka Cika Harabar ATM

Rahotonni da ke ci gaba da shigo muna yanzu haka, na nuni da cewa ɗaruruwan mutane na ta yi dogayen  layuka a gaban na'urar cirar kuɗi ta ATM da ke bankuna, inda suke amfani da wani salo na biyan mutane domin su ciro mu su kuɗi.
Wani da muka zanta da shi mai suna Lawal Mai Masara, ya shaida muna cewa, tun jiya ya ke kan layi, kuma har yanzu bai kai ga samun kuɗin ba saboda masu sana'ar POS da masu kwashe kuɗi su sake adanawa sun cika ko'ina.
"Za ka ga mutane riƙe da katunan cirar kuɗi fiye da 10 inda suke tura ma wasu kuɗi su rarraba musu katunan domin a cire mu su kuɗin a ATM daga baya su bayar da naira dubu akan duk dubu goma da aka cire mu su". In ji shi.
Mutumin ya ƙara da cewa wannan na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa ƙarancin kuɗi tsakanin mutane a Najeriya.musamman arewa.

Wannan sabon matakin ya nuna irin yadda mutane ke jefa kansu a halin tasku ta hanyar ci gaba da kwashe kuɗaɗen da jama'a ya kamata su samu.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ya zama wajibi hukumomin tsaro sau ɗauki matakin yi wa tufkar hanci muddin ana son a samu sauƙi a rayuwa.

"Ta ya za a samu sauƙi bayan mutane sun mayar da kansu 'yan-jari-hujja?
Kuma a haka ake neman samun shugabanni na gari bayan kowa ya zama maketacin ɗan'uwansa". In ji shi.

Comments