A daidai lokacin da ake daf da rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden, an baza dubban jami'an tsaron soji domin murkushe duk wata zanga-zanga da ka iya barkewa. Tun a farkon makon da ya gabata ne dai Hukumar Leken Asiri ta Amurka ta FBI, ta yi gargadin cewa akwai yuwar samun tarzoma a ko'ina a kasar. Zababben shugaban dai ya shawarci jama'a da su yi zaman su a gida ba sai sun halarci bukin rantsarwar ba, ko baya ga matsalar annobar korona akwai yuwar dakarun sojin da aka baza na shirin maganin duk wanda ya nemi daukar dala ba gammo. Shugaba Donald Trump mai barin gado ya bayyana cewa zai bar babban birnin kasar Washington DC tun da sanyin safiyar gobe laraba, don kaucewa yin ido biyu da wanda zai gaje shi. A tarihin kasar dai wannan ne karon farko da za a yi bukin rantsarwa mafi tsaurin tsaro a Amurka, da kuma armashinsa ya ragu, muddin ta tabbata bai samu halarcin jama'a ba.