Skip to main content

Daliban Jahar Sokoto Ba Zasu Rubuta Jarabawar WAEC Ba


Hukumar Shirya Jarabawar Sakandire ta Afirka ta Yamma wato WAEC, ta bayyana cewa jahohin Sokoto da Zamfara ba su aike mata da sunayen dalibansu da za su rubuta jarabbawar kammala babbar sakandire ba, wadda za a soma tsakanin ranakun 16 zuwa 23 ga watan Yunin gobe, kamar yadda sakataren hukumar shirya jarabawar Mista Patrick Aregan ya fitar da sanarwa.

Sai dai a hirarsa da Sashen Hausa na BBC, kwamishinan ilmi na jahar Sokoto Bello Abubakar Guiwa, ya ce matsalar ba daga gare su ba ne. 
Kwamishinan ya ce hukumar ta WAEC ta fito ne da wani tsari na sun amsar kudi ba gaira ba dalili gare su wanda ya sa suka yi watsi da ita.
Ya kara da cewa suna da dalibai kusan 30,000 da zasu rubuta jarabawa a wannan shekara, to amma sai hukumar hana su lambobin jarabawar da ake rabawa dalibai ta kuma ce duk wani kuskure daya da aka samu akan kowane dalibi, wajibi ne sai an biya naira 5000, wanda kuma miliyoyin kudade ne, kazalika sai gwamnatin jahar Sokoto ta biya kashi 40 cikin dari kafin somawa.
Da aka tambai shi ko akwai yuwar sasantawa kan wannan batu, sai ya ce, "Kamar yaya sansantawa wai, muna da matsala ne? Batun ya za a yi ai bai taso ba, kasuwanci ne, WAEC shago ne, idan suna so su zo mu shirya mu ci gaba kasuwanci".

To sai dai ba wannan ne karo na farko ba da jahar Sokoto ke zama sahun baya wajen rubuta jarrabawar ta WAEC ba, in da ko shekarar bara daliban jahar sun rubuta jarabowoyin NECO da NABTEB. Abinda kuma ake gani kamar wani koma baya ne a bangaren ilmi dik kuwa da dokar ta baci da gwamnan jahar Aminu Waziri Tambuwal ya saka, ga kuma shi an buga tambarin siyasa yana kuma daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa.

Sai ku danna hoton da ke kasa don ku saurari kalaman kwamishin ilmin jahar Sokoto
Credit: BBC Hausa



Comments