Lamarin ya kazance ne bayan da wasu daga daliban kwalejin suka yi zargin cewa ta dade ta na wannan batancin abinda ya kai ga barkewar rikicin da ya kai ga salwantar ranta.
Tuni dai mahukuntan jahar Sokoto suka bayar da sanarwar rufe kwalejin har a kammala bincike. Babban sakatare a ma'aikatar ilmi mai zurfi ta jahar Sokoto Alhaji Almustapha Usman Ali, ya shaidawa manema labarai cewa, an bayar da umurnin rufe kwalejin kazalika za su sanar da jama'a mataki na gaba idan har an kammala bincike.
An dai girke jami'an tsaro a harabar makarantar domin dakile rikicin da ka iya tasowa.
Tuni dai da hotunan bidiyo da Tantabara ba ta kai ga tantantace sahihancinsu ba, suka karade shafukan sada zumunta, wadanda ke nuna dalibar kwance wasu na dukan ta tare da cewa a sa ma ta wuta.
Comments