Skip to main content

ASUU Ta Tsunduma Sabon Yajin Aikin Watanni Uku

Kungiyar Malaman Jami'a ASUU ta fitar da wata sabuwar sanarwa a yau litinini 09/05/2022 da ta bayyana sake tsunduma wani sabon yajin aikin makonni 12.

ASUU ta bayyana rashin gamsuwa da yadda bangaren gwamnatin tarayya ya dauki lamarin ba tare da muhimmanci ba. Sanarwar ta ASUU ta kuma nunar da yadda gwamnatin tarayya ta sa kafa ta shure yarjejeniyar da suka yi a 2020, tare da cewa babu wata alamar gwamnati da gaske ta ke.

Kungiyar Malaman Jami'ar dai ta kwashe wata hudu tana yajin aiki kafin sake saka wani sabon wa'adi a yau na tsawon makonni 12 abinda masana harkar ilmi ke cewa ya gurgunta sha'anin ilmi a Najeriya.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey