Skip to main content

Zan Yi Amfani Da Kundin Tsarin Mulki Ba Alkur'ani Ba - Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jahar Zamfara sanata Sani Yariman Bakura ya ayyana manufarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar APC.
A wata hira da BBC Hausa Yariman Bakura ya bayyana cewa Najeriya na fama da matsaloli uku da zai mayarwa hankali idan aka zabe shi, da suka hada da tsaro da jahilci da talauci.
Da aka tambai shi ko bai ganin wadanda ba musulmi ba na iya dari dari a zabensa. Sai ya ce a yanzu kam sabanin wancan lokaci da aka sani da kundin tsarin mulki zai yi amfani wajen rantsuwar kare Najeriya. Ya kuma kara da cewa a lokacin kaddamar da manufar tsayawarsa takara akwai limaman kiristoci daga Zamfara da wasu wurare a Najeriya da suka halarta, wanda alama ce da ke nuna zai yi ma kowa adalci a cewar sa.

Sanata Sani Yariman Bakura dai shi ne gwamna na farko da ya assasa shari'ar Musulunci a jahar Zamfara a shekarar 2000. Wanda daga baya aka samu jahohin Sokoto da Kano suka bi sahu. 
Abinda ya jawo karo na farko a tarihi gwamnatin jahar Zamfara ta fara zartar da hukuncin sare hannu, da aka yi ma wani da ake kira Buba Kare Garke da aka zarga satar saniya, sai kuma wata da aka yankewa hukuncin rajamu (jefewa) mai suna Safiya Hussaini Birnin Tudu, da ita ma aka zarga da aikata zina.
A wannan karon Sanata Yarima ya bayyana cewa da kundin tsarin mulkin Najeriya zai yi aiki ba da Al'kur'ani ba.
Da aka tambai shi game da sayen fom din takara da ya kai naira miliyan 100, ya ce shi kam ba shi da kudi amma dai abokan arziki da sauran kungiyoyin da ke goyon bayan takararsa ne za su saya masa. 

Comments

ALHUDA-HUDA said…
Tooo! Wani sabon salo gemu a kafada