Skip to main content

Zan Yi Amfani Da Kundin Tsarin Mulki Ba Alkur'ani Ba - Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jahar Zamfara sanata Sani Yariman Bakura ya ayyana manufarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar APC.
A wata hira da BBC Hausa Yariman Bakura ya bayyana cewa Najeriya na fama da matsaloli uku da zai mayarwa hankali idan aka zabe shi, da suka hada da tsaro da jahilci da talauci.
Da aka tambai shi ko bai ganin wadanda ba musulmi ba na iya dari dari a zabensa. Sai ya ce a yanzu kam sabanin wancan lokaci da aka sani da kundin tsarin mulki zai yi amfani wajen rantsuwar kare Najeriya. Ya kuma kara da cewa a lokacin kaddamar da manufar tsayawarsa takara akwai limaman kiristoci daga Zamfara da wasu wurare a Najeriya da suka halarta, wanda alama ce da ke nuna zai yi ma kowa adalci a cewar sa.

Sanata Sani Yariman Bakura dai shi ne gwamna na farko da ya assasa shari'ar Musulunci a jahar Zamfara a shekarar 2000. Wanda daga baya aka samu jahohin Sokoto da Kano suka bi sahu. 
Abinda ya jawo karo na farko a tarihi gwamnatin jahar Zamfara ta fara zartar da hukuncin sare hannu, da aka yi ma wani da ake kira Buba Kare Garke da aka zarga satar saniya, sai kuma wata da aka yankewa hukuncin rajamu (jefewa) mai suna Safiya Hussaini Birnin Tudu, da ita ma aka zarga da aikata zina.
A wannan karon Sanata Yarima ya bayyana cewa da kundin tsarin mulkin Najeriya zai yi aiki ba da Al'kur'ani ba.
Da aka tambai shi game da sayen fom din takara da ya kai naira miliyan 100, ya ce shi kam ba shi da kudi amma dai abokan arziki da sauran kungiyoyin da ke goyon bayan takararsa ne za su saya masa. 

Comments

ALHUDA-HUDA said…
Tooo! Wani sabon salo gemu a kafada

Wadanda aka fi karantawa

Breaking: Chadian President Idris Deby Is Dead

  Chadian President Idris Deby died while leading the country's security forces over the weekend, fighting rebels on the northern country's border with Libya.  President Deby is widely expected to win the country's general election by 80 percent after seeking a sixth term.  The military has dissolved parliament and announced that it would hold power for 18 months before new elections.  Idris Deby took power in Chad in 1990 after overthrowing the government of former President Hissene Habry, and has ruled Chad for 30 years.

Wata Mota Cike Da Harsasan Bindiga Ta Fada Rami A Garin Awka Na Jahar Imo

Hankalin jama'a yayi matukar tashi a jiya Lahadi biyo bayan gano wata babbar mota cike da harsasai masu rai a birnin Anacha na jahar Imo da ke kudu maso gabashin tarayyar Najeriya. Rahotannin da suka shigo muna na cewa jami'an tsaron cikin hanzari sun afkawa garin na kasuwanci domin daukar matakin gaggawa kan lamarin.  Babbar motar wadda ke dauke da kwaliyoyin harsasai masu rai ta fada cikin wani rami da ke kan titi, inda dukan harsasan suka zube. Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce: “Motar ta fadi, kuma duk titin na cike da harsasai.  Wasu yaran ma sun debi wasu da hannayensu suka gudu, kafin jami’an tsaro su iso wurin. ”  Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa direban babbar motar da mai yi masa hidima sun yi watsi da motar bayan hatsarin ya faru, inda suka yi batan dabo zuwa inda ba a sani ba. Amma wata majiyar ta ce ‘yan sanda sun cafke direban. “Lamarin ya jawo jami'an tsaro masu yawa zuwa yankin hanyar Awka da da safiyar yau. 'Yan sanda sun...

Stepping Down Not The Right Option - Osinbajo

Vice president Yemi Osinbajo has denied reports that he intends to step down for a certain presidential aspirant ahead of the presidential primary of the All Progressives Congress (APC). The denial is contained in a statement by the chairman of Osinbajo’s campaign council, Richard Akinnola on Sunday. According to the statement, the people behind the speculation are “afraid of the huge political support base of the Vice President, Prof. Yemi Osinbajo,” adding that the VP is ready for the presidential primary scheduled to hold between June 6 and 8. The campaign council “welcomes our distinguished delegates from across the country to Abuja for our presidential primaries. “As you settle down in Abuja, we implore you to kindly disregard various fake news making the rounds that Prof. Yemi Osinbajo has stepped down. “Osinbajo would be hoping to clinch the ticket of the ruling party with much desire to take over from his principal, President Muhammadu Buhari at the end of his tenur...

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidajen Ma'aikatan Filayen Jiragen Saman Najeria Tare Da Sace Mutum 11

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari a gidajen ma'aikatan Hukumar Filin Jirgin Saman Tarayyar Najeriya da ke Kaduna, inda suka yi awon gaba da akalla mutane 11. Rahotannin baya-bayan nan sun kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi nasarar sace ma’aikacin Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA)A, da matarsa, da jami’in Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIMET) da ya’yansa, kuma har yanzu ba a san inda suke ba. Satar mutane ya zama ruwan dare a Najeriya a yau, kuma kusan kowace safiya ana samun rahotannin kashe-kashe ko satar mutane don neman kudin fansa.  A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen satar mutane a Najeriya amma ga dukkan alamu kalaman nasa ba su yi tasiri ba. 

Gunmen Abducted 11 FAAN Staff In Kaduna

A group of gunmen yesterday attacked the residences of the Federal Airport Authority of Nigeria Kaduna. Reports say gunmen stormed the compound and abducted at least 11 people. Recent reports suggest that the bandits also abducted a staff of  Nigerian Airspace Management Agency NAMA, his wife, a National Meteorological Agency (NIMET) official and his children.Their whereabouts are still unknown. Kidnappings are common in Nigeria today, and almost every morning there are reports of killings or kidnappings for ransom. Last week Nigerian President Muhammadu Buhari vowed to end abduction in Nigeria but for all indications his words were not effective.

PDP Na Shirin Korar Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya shigar da ƙara domin hana wani sabon yunƙurin jam’iyyar PDP dakatar da shi daga cikinta, kuma ya buƙaci kotun da ta ɗauki mataki ga duk masu wannan aniya.  Ɗaya daga cikin jigajigan jam'iyyar PDP da suka mayar da martani kan ƙarar da gwamna Wike ya shigar, Mahdi Shehu, ya mayar da martani a ranar Litinin da ta gabata inda ya wallafa a shafinsa na twitter wata sanarwa cewa, “Wike ya shigar da ƙara kan jam’iyyar PDP mai lamba FHC/ABJ/CS/139/2023 ta hannun lauyoyinsa, DY Musa (SAN);  Douglas Moru, da C. C. Chibuike, yana neman a ba shi umarnin hana a kore shi daga PDP.”   Wike dai ya yi ta famar ruguza jam’iyyar har ma ya rasa inda za shi. Gwamnan na Ribas ya zamewa jam'iyyar PDP ƙadangaren bakin tulu, irin yadda ya ke uwa da makarbiya tun bayan da dangantaka ta soma tsami tsakaninsa da wasu jigajigan jam'iyyar ciki kuwa har da gwamnan jahar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.  

Farkawar Matan Afirka

Afirka nahiya ce mai dogon tarihi. Tun asali,  yawancin Turawa sun yi kokarin sanya idanu a kan nahiyar, sun ziyarce ta don neman ko dai kasuwanci, wanda a wancan lokacin wani nau'i ne na cinikin bayi ko kuma daga baya ya koma ga cinikin kayan masarufi kamar su gyada, auduga, fatun dabbobi da makamantansu. Zuwan Larabawa kuma, a wasu lardunan Afirka na lokacin, gami da yankin da ake kira "Sudaniyya", wanda ya hada da Sudan, Najeriya, Chadi, da wasu sassan Jamhuriyar Nijar, ya haifar da yaduwar Musulunci da al'adun Gabas. Daga baya, zuwan Bature ya kawo kiristanci, ilimin yamma da sauran manufofin Turawa. Nahiyar Afirka sannu a hankali tana juyawa zuwa matakai daban-daban; daga duhun kai har zuwa halin da ake ciki a yau. Ilimin addini da na zamani sun samu gindin zama a kasashen Afirka, amma har yanzu mata suna baya a wannan tafiyar. Sau da yawa za ka ga mata a yankunan karkara har ma da wasu biranen Afirka ci...

Filin Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Zai Ci Naira Biliyan 700

Ministan suhurin jiragen sama Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa majalisar zartaswata ƙasa ta amince da ware fiye da naira biliyan ɗari bakwai domin aikin kwangilar gyaran filin sauka da tashin jiragen na sama na duniya na Malam Aminu Kano, wanda ya ce za kammala a cikin shekara ɗaya rak. Majalisar zartaswa ta ƙasa ta kuma amince da ware naira biliyan ɗari da goma sha bakwai domin gudanar da kwangilar gina cibiyar bincike akan man fetur ta Oloibir a yankin Naija Delta. Ministan ƙasa a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya shaidawa ‘yan jaridar fadar shugaban ƙasa hakan, inda ya ce za a kammala aikin kwangilar a cikin shekaru biyu da rabi. Ya ce tun a 1980 gwamnatin Alhaji Shehu Aliyu Shagari ta soma aikin, amma daga bisani aka yi watsi da shi wanda a yanzu zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za a ci ga da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Dalar Amurka Na Fuskantar Barazanar Durkushewa

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya soki kasar Amurka akan irin rawar da dala ke takawa a tattalin arzikin duniya tare da yin kakkausar suka ga asusun lamuni na duniya na IMF. Lula ya yi waɗannan kalamai a wata ziyarar aiki da ya kai Chana, jiya Alhamis a birnin Shanghai a wani bikin kaddamar da takwaransa, Dilma Rousseff a matsayin sabuwar shugabar bankin raya kasashen BRICS, da gamayyar kasashenn Brazil da Rasha da Indiya da Chana da kuma Afirka ta Kudu suka samar. "Me ya sa kowace ƙasa za a danganta da dala don kasuwanci? Wanene ya yanke shawarar dala za ta zama kuɗin duniya?"  Ya ƙara da cewa me yasa banki kamar bankin BRICS ba zai iya samun kuɗin da zai gudanar da hulɗar kasuwanci tsakanin Brazil da Chana ba, da ma sauran ƙasashen duniya? Ya ce yana mamakin yadda ƙasashe cike da rauni  su ke bin sawun amfani da dala wajen gudanar da kasuwanci alhali suna iya hakan da kuɗaɗensu. A wata ganawa tsakanin sa da shugaban Chana Xi Jinping, da kuma ya ...

Nigerian President Vaccinated Against Covid-19

Nigerian President Muhammadu Buhari and his vice president, Professor Yemi Osinbajo, have been vaccinated with AstraZeneca vaccine, just one day after the nationwide vaccination campaign. Earlier, the Federal Government announced that as soon as the vaccine arrives in Nigeria, the President, government officials and all Governors will be at the forefront of the immunization drive which would be shown on the National Television (NTA) to set an example for other Nigerians, as well as allay their fears about the legitimacy of the vaccine. The president's doctor, Dr. Shuaibu Rafindadi, vaccinated the president at 11:53 a.m. Nigerian time (10:53 a.m. GMT) on Saturday, and Vice President Yemi Osinbajo immediately joined the process. They were also provided with electronic immunization cards by the Director General of Primary Health Care Development (NPHCDA), Dr. Faisal Shuaib. Nigeria successfully started the vaccination on Tuesday, becoming the third West African country to ...