Skip to main content

Binani Na Neman Kotu Ta Tabbatar Da Ita Wadda Ta Lashe Zaɓen Adamawa

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa a ranar Litinin sun fito kan tituna domin nuna adawa da ayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa.
Sai dai ita Binani ta buƙaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daga sauya matakin da aka ɗauka na ayyana ta da a ka yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen.
 A wata buƙata da ta shigar a ranar Litinin, mai neman izinin kotun ya nemi izinin kotun ta ba ta damar shigar da buƙatar neman umarnin haramtawa INEC daga ɗaukar duk wani mataki na watsi da sanarwar da aka yi a ranar 16 ga Afrilu da Kwamishinan zaɓen jahar, Barista Hudu Ari ya ayyana ta a matsayin wadda ta samu ƙuri'u mafifi rinjaye kuma ta lashe zaɓen alhali ba a kammala tattara sakamakon zaɓen gaba ɗaya ba.
Ta kuma nemi a ba da umarnin hana hukumar zabe ta INEC, da wakilinta nadawa ko kuma duk wanda ke wakiltarta daukar wasu matakai na bayyana wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da kuma karin zaben da aka gudanar a ranar 15 ga Afrilu, har sai kotun tayanke hukunci tukuna. 
Hukumar ta INEC dai tuni ta dakatar da kwamishinan zaɓenta na jahar Adamawa saboda matakin da ya ɗauka na ayyana ta a matsayin wadda ta samu nasara ba tare da kammala tattara sakamako ba.

 A ɗaya daga cikin dalilan da ta shigar da ƙarar, Binani ta ce kotu ɗaya tilo ke da hurumin nazarin bayyana sakamakon zaɓen ita ce kotun sauraron kararrakin zaɓe ta ƙasa.

Ta ƙara da cewa duk ɗan takarar da bai gamsu da sakamakon ba, to ya na da damar garzayawa kotun ƙoli domin neman hakkinsa.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.