Skip to main content

Ko Kun San Yadda Gidajen Samudawa Su Ke?

Samudawa su ne mutanen Annabi Saleh (AS) waɗanda ke da girman jiki da tsawo tamkar bishiyar dabino.
 
Waɗannan wasu daga gidajen Samudawa ne da suka rage a halin yanzu. Ana kiran wajen da suna (Mada’in Salih) ko Al-Hijr da Larabci,  (ٱلْحِجْر‎‎). Yankin na nan a Al-‘Ula cikin lardin Madina a Hejaz, ta ƙasar Saudiyya.
A shekarar 2008, Hukumar Kula Da Adana Kayan Tarihi Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ayyana Mada’in Salih a matsayin wani wajen da take girmamawa, wurin tarihi na Hegra na nan nisan kilomita 20 arewa da garin Al-‘Ula, tafiyar mil 250 arewa maso yammacin birnin Madina.
Samudawa sun wanzu shekaru ɗari bakwai da goma sha biyar kafin haihuwar Annabi Isa (AS).
Mutane daga sassa daban-daban na duniya kan ziyarci wurin, domin ganin ikon Allah.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey