Skip to main content

Tsaunin Hin Sam Wan Mai Ɗimbin Shekaru A Duniya

Tsaunukan Hin Sam Wan, da kuma aka fi sani da Dutsen Whale Uku, wasu tsaunuka ne ma su ban sha'awa da suka kai kimanin shekaru miliyan 75. 
Suna cikin daga tsaunukan ƙasar Thailand masu ban mamaki.  Sunansu ya samo asali ne daga kamanninsa, idan aka dubi tsaunin daga sama daga sama za a ga ya yi kama da dangin whales wato dabbar nan ta tekun mai kama da kifi whale.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.