Skip to main content

Zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto A Jam'iyyar PDP Ya Bar Baya Da Kura


Bayan da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci zaman sulhu domin tsayar da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP tare da zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma, hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin jama'a.

Daga cikin jerin 'yan takarar da suka nemi kujerar akwai mataimakin gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Maniru Muhammed Daniya da kwamishin muhalli na jahar Sokoto, Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa da tsohon sakataren gwamnatin jahar Sokoto, Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma da kuma tsohon mataimakin gwamnan jahar Sokoto Alhaji Muktari Shagari.

Bayan zama da gwaman Aminu Waziri Tambuwal ya yi da dukan su a dakin taro na kasa da kasa da ke Kasarawa, daga karshe gwamnan ya tabbatar da Sa'idu Umar Ubandoma a matsayin wanda zai yi ma jam'iyyar PDP takarar gwamna a 2023.

Rahotannin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da cewa shi ma daya daga 'yan takarar da bai yi nasara ba, Alhaji Muntari Shagari ya fice daga jam'iyar ta PDP sai dai bai bayyana in da zai koma ba, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Ina son sanar da magoya bayana cewa daga yau na fice daga jam'iyar PDP domin kyakkyawar manufa. Zan sanar da matakin da zan dauka nan gaba."
Sabuwar zanga-zangar da aka soma ta karade wurare da dama a Sokoto, in da su ke bayyana rashin amincewa da zabin da suka ta'allaka ga gwamna Tambuwal tare da yin kalamai masu zafi, kamar yadda wani shi ma mai suna Shamsu Ibrahim ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook.
Wani shi ma mai suna Zaharaddeen Photos Hamma'ali ya wallafa bidiyo makamancin wannan, in da ake jin wata murya na cewa za su bar Tambuwal su bi Atiku.
Ku dannan kafar da ke kasa don ganin bidiyon biyu:






Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey