Skip to main content

Filin Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Zai Ci Naira Biliyan 700

Ministan suhurin jiragen sama Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa majalisar zartaswata ƙasa ta amince da ware fiye da naira biliyan ɗari bakwai domin aikin kwangilar gyaran filin sauka da tashin jiragen na sama na duniya na Malam Aminu Kano, wanda ya ce za kammala a cikin shekara ɗaya rak.
Majalisar zartaswa ta ƙasa ta kuma amince da ware naira biliyan ɗari da goma sha bakwai domin gudanar da kwangilar gina cibiyar bincike akan man fetur ta Oloibir a yankin Naija Delta.
Ministan ƙasa a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya shaidawa ‘yan jaridar fadar shugaban ƙasa hakan, inda ya ce za a kammala aikin kwangilar a cikin shekaru biyu da rabi.
Ya ce tun a 1980 gwamnatin Alhaji Shehu Aliyu Shagari ta soma aikin, amma daga bisani aka yi watsi da shi wanda a yanzu zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za a ci ga da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.


Comments

Wadanda aka fi karantawa

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey