Skip to main content

An Gano Wani Rini Na Zamanin Annabi Dawuda

Wata jaridar kasar Isra'ila mai suna Hamodia ta wallafa labarin mai ban mamaki da ya ja hankalin duniya a makon nan.
Masu hakar kayan tarihi da hadin guiwa da Jami'ar Barllan da kuma Jami'ar birnin Tel-Aviv ne suka samu nasarar gano wannan rinin mai lainin shudi, da shuni hade da saheti da aka ce ya kai shekaru dubu daya kafin bayyanar annabi Isa (a.s.) da kuma mazauna wani kwari da ake kira Slaves Hill da ke lardin Timna ke rinawa a lokacin.
Wani masani na Jami'ar Barllan Dakta Naama Sukenik da Dakta Erez Ben-Yosef, sun bayyana cewa rinin, mai matukar darajar gaske an samar da kayan hadinsa ne daga kwanson dodon kodi. Kuma an wallafa bayanin a mujallar PLOS ONE.

Comments

Unknown saidā€¦
Abin mamaki baya karewa a Duniya.
Unknown saidā€¦
Wow!Wonders never end.

Wadanda aka fi karantawa

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.