Skip to main content

An Gano Wani Rini Na Zamanin Annabi Dawuda

Wata jaridar kasar Isra'ila mai suna Hamodia ta wallafa labarin mai ban mamaki da ya ja hankalin duniya a makon nan.
Masu hakar kayan tarihi da hadin guiwa da Jami'ar Barllan da kuma Jami'ar birnin Tel-Aviv ne suka samu nasarar gano wannan rinin mai lainin shudi, da shuni hade da saheti da aka ce ya kai shekaru dubu daya kafin bayyanar annabi Isa (a.s.) da kuma mazauna wani kwari da ake kira Slaves Hill da ke lardin Timna ke rinawa a lokacin.
Wani masani na Jami'ar Barllan Dakta Naama Sukenik da Dakta Erez Ben-Yosef, sun bayyana cewa rinin, mai matukar darajar gaske an samar da kayan hadinsa ne daga kwanson dodon kodi. Kuma an wallafa bayanin a mujallar PLOS ONE.

Comments

Unknown said…
Abin mamaki baya karewa a Duniya.
Unknown said…
Wow!Wonders never end.

Wadanda aka fi karantawa

Abduljabbari Ya Kasa Kare Kansa

Shugaban Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami'ar Bayaro da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace baya ga kame-kame da Abduljabbar ke yi babu wata tambaya daya tak da ya amsa. Ya kara da cewa a maimakon ya bude wagagen littafan nan da ya zo da su don fiddo da hujja sai kawai ya ce babu lokaci. A kan hala ya yanke hukuncin cewa Abduljabbar Nasiru Kabara ya kasa kare kansa. A na sa bangare Abduljabbar ya nemi a dai sake ba shi wani lokaci, watakila idan ya shirya, kuma ga hujja, zai iya tuba. Sai dai Malam Abubakar Madatai, daya daga masu gudanar da muhawarar, ya roki a sake ba Abduljabbar karin lokacin ya ke ta bukata. Su sun shirya amma ya ce shi bai shirya ba don haka a ba shi karin lokacin, kazalika ya nemi gwamnatin jahar Kano da nan gaba idan an amince da bukatar to a bada damar watsawa a gidajen rediyo da talabijin kowa ya ji ya gani.

Abduljabbari Ya Ce Idan An Ba Shi Sarari Zai Tuba

 Abduljabbari ya koka a kan yadda mukabalar ke tafiya, duk da ya kasa amsa muhimman tambayoyin da aka yi masa. Ya ce mintina 10 da aka ba shi don ya amsa tambayoyin da suka shafi cin zarafin Annabi (s.a.w.) ba za su isa ya kwance littafai kusan 500 da ya zo da su ba. An tambai shi ko a wane hadisi aka kira annabi bunsuru ko arne? Ya ce idan an ba shi karin lokaci zai binciko hadisan ya zo da su amma yanzu an kure shi ba cikin shiri yake ba, kuma gaba daya a cewar sa, babu gaskiya a mukabalar. Ya ce yana son ne ya tsamo mutane daga halakar da ke sa suna yin ridda sakamako rudanin hadisan. Kasancewar wannan kasawa ya sa daya daga Malaman da ke zurara masa tambayoyi Malam Abubakar Madatai ya neme shi da ya tuba ya tabbatar da kuskuren da ya yi. Amma Abduljabbar ya ce ta ya zai tuba a wajen wannan muƙabala, a gaban kowa da kowa, ba tare da ba shi karin lokaci don haduwa ta gaba ba, sannan a ba shi karin wasu hujjoji da suka fi nasa.  Da ya ki tuba, malamin na bangar

Ba Za Kara Sace Kowa Ba A Najeriya - Inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen ci gaba da satar jama'a a fadin Najeriya. An dai jiyo hakan ne a ta bakin Ministan sufurin jiragen sama na kasa, Sanata Hadi Sirika lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin tarayya don yiwa gwamnatin jahar Zamfara jaje, akan daliban Makarantar Kimiyya ta 'Yan Mata ta Jangebe su kimanin 300 da aka sace. Sirika ya ce wannan shi ne na karshe, domin kuwa gwamnatin tarayya za ta dauki sabbin matakai da za su taimaka wajen dakushe ayukkan ta'addanci da suka mamaye yankunan arewa. Ya kara da cewa Buhari ya nuna damuwarsa matuna kan yadda ayukkan ta'addanci ke dada raruwa. Shugaban kasar ya kuma yabawa gwamnan jahar Zamfara saboda kokarinsa wajen yaki da matsalar tsaro. Shi ma gwamnan jahar Zamfara, Bello Mutawalle ya bayyana jin dadi akan yadda gwanatin tarayya ke nuna kulawarta akan wannan lamari.

Barista Yunusa Ari Ya Yi Ɓatan Dabo

Dakataccen kwamishin hukumar zaɓe na jahar Adamawa, Barista Yunusa Hudu Ari, ya ranta cikin na kare jim kaɗan bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi a gudanar da cikakken bincike game da badaƙalar da ake zargin sa da ita. Kakakin hukumar INEC Festus Okoye ne ya sanar da gidan talabijin na Channels haka. Okoye ya ce su kansu ba za su iya cewa ina ya shiga ba saboda tun bayan faruwar lamarin ba ya ɗaukar kiran waya kuma sun ma daina jin ɗuriyarsa gaba ɗaya. Da aka tambai shi ko akwai wani mataki da hukumar INEC za ta ɗauka kan wannan sabon lamari, sai ya ce, "ai wannan hakkin jami'an tsaron 'yan sanda ne na tabbatar da sun san inda yake. Idan har jami'an tsaro na buƙatar gurfanar da shi, su ne za su iya zaƙulo shi tare da gabatar da shi a gaban shari'a". Hudu Ari dai ya sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jahar Adamawa a ranar Lahadin makon jiya, inda ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun gabanin a kammala tat

No More Abduction In Nigeria - Says Buhari

Nigerian President Muhammadu Buhari has assured Nigerians that abduction of 300 female students from Government Girls Science Secondary School, Jangebe, Zamfara State, would be the last to happen in the country. Minister of Aviation, Senator Hadi Sirika, conveyed Buhari’s declaration when he led a high-powered federal government delegation to sympathise with the people and government of Zamfara State. According to him, 'Buhari is assuring the citizens there would be no abduction again because the Federal Government would show its commitment in fighting banditry and other forms of insecurity in the country’.  The minister said new measures have been developed by the federal government which would bring complete end to all forms of criminality in the nation. Sirika said the president is agitated by the setback and increase of banditry in almost everywhere in the north, which he noted that would not be tolerated. Buhari also commends zamfara State Governor, Bello Matawalle

Littafan Da Abduljabbari Ya Nemi Ya Karanto A Wurin Mukabalar Da Ta Gabata

National Directorate of Employment (NDE) Disburses 100,000 as a Loan to 108 Agricultural Empowerment Scheme Beneficiaries in Sokoto

The state Coordinator of the agency said this was to enable the beneficiaries to be self reliant and contribute their quota to the development of the country. She said the programme was a combined orientation made up of 108 beneficiaries of Agricultural Empowerment Scheme, Community Based Agricultural Empowerment Scheme, Sustainable Agricultural Development Empowerment Scheme and Graduate Agricultural Empowerment Scheme that were given loans of N100, 000 each. Mrs. Danmallam added that the beneficiaries are graduates of NDE agricultural Extension, Poultry and Vegetable production. She said the money disbursed to them was a loan facility which would attract a single digit simple interest rate of 9 % and will have a moratorium of six months before beneficiaries will start paying back and it is repayable in three years.  Therefore, urged the them to ensure timely repayment to enable other unemployed persons to also benefit. In his goodwill message, repr

Ba Kan Mu Aka Fara Ba - 'Yan Majalisar Zamfara

Gwamnatin jahar Zamfara ta sa kafa ta yi fatali da umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na hana shawagin jiragen sama a duk fadin jahar. 'Yan majalisar jahar sun yi kukan kura in da suka kada kuri'ar kin amincewa da wannan mataki da suka bayyana da ihu-bayan-hari. Daya daga mahunkuntan da ya fito da kudirin har ya samu amincewa, Faruku Dosara yayi terere wa gwamnatin tarayya tare da raddi ga mai ba shugaba Buhari shawara kan lamurran tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya, dangane da sakaci da ya zarge shi da yi kan lamurran da suka shafi tsaro da hukunta wadanda ake zargi da hannu ga sha'anin. Kwanan nan dai ne aka yi garkuwa da daliban makarantar Sakandiren Kimiyya ta Jangebe su kimanin 300 da suka shafe kwanaki a hannun 'yan bindiga kafin sakin su, abinda masana ke zargin sai da aka biya kudin fansa kafin a cimma yarjejeniyar, lamarin da zai iya ci gaba da dagula matsalar tsaro a Najeriya. Faruku Dosara ya ce, "ai ba

Buhari Ya Amince A Kashe Tsohuwar Naira 200

A wani jawabi da ya yi a yau Alhamis, shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya ba Babban Bankin Najeriya CBN umurnin sake fito da tsohuwar naira 200 a hannun al'umma domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun wannan shekara. Buhari ya bayyana cewa an samu muhimman nasarori ta dalilin canjin fasalin kuɗi da aka yi. Ya nunar da cewa yana sane da irin halin matsin da 'yan Najeriya suka shiga, akan haka suna iya amfani da tsohuwar naira 200 sai dai su kai tsofaffin kuɗaɗe da suka haɗa da naira 500 da kuma naira 1000 a bankin CBN. Menene ra'ayinku kan wannan batu?

92 Feared Dead As Oil Tanker Explodes in Sierra Leone

A huge oil tanker explodes in Sierra Leone's capital;  more than 90 people are feared dead.  Many people were injured, and most were seriously injured.  Local reports say Freetown hospitals are overcrowded.  The bomber struck shortly after noon in front of a petrol tanker.  Pictures posted on social media showed the blaze burning at the scene as the fuel spread, with several cars burning and causing an explosion.  The chairman of the National Emergency Management Agency, Lieutenant-General Brima Sesay, described the situation as "extremely serious" and said the bodies had been burnt. Bashir Ahmad Zubairu is a multi-media journalist in Nigeria Email: bashir.visionfmradio@gmail.com